Wednesday, 31 October 2018

Bata lokacine kai Buhari kotu saboda maganar takardun makarantarshi>>Fadar shugaban kasa

Tun a zaben shekarar 2015 aka yi ta cece-kuce akan takardun makarantar shugaban kasa, Muhammadu Buhari yayin da yace takardun nashi na tare da hukumar soji takasa wadda yayi aiki da ita ya kuma yi ritaya a matsayin Majo janar.


A wancan lokacin sojin sun musanta waccan magana inda har wasu 'yan Najeriya suka shiga kotu akan a hana Buharin takara kan wannan lamari, daga baya da ya ci zabe sun janye karar inda suka ce an musu barazanar cewa idan basu janye ba za'a ci zarafinsu

A wannan karin ma da shugaba Buharin ke neman zarcewa ya bayyanawa hukumar zabe cewa har yanzu fa takardunshi na tare da hukumar soji daga bayana fadar shugaban kasar ta fito tace hukumar sojin sun ce takardun na shugaban kasa fa sun bata.

Jaridar Thisday ta ruwaito cewa jam'iyyar PDP da wani mutum me suna, Itsede Kingley sun maka Buharin a kotu akan dai wannan batu.

Saidai me magana da yawun shugaban kasa, Malam Garba Shehu ya bayyana cewa maganar ta takardun makarantar Buhari an gamata, sake kai maganar kotu bata lokacine da abin kunya da kuma wasa da hankalin shari'a.

No comments:

Post a Comment