Saturday, 27 October 2018

BBC ta karrama taurarin Hikayata na 2018

BBC ta karrama taurarin Hikayata na bana a ranar Juma'a a Abuja.

A watan Satumba ne alkalan Gasar Rubutun Gajerun Labarai ta Mata ta BBC Hausa, wato Hikayata, sun bayyana ''Ya Mace', a matsayin labarin da ya yi zarra cikin labarai sama da 300.


Wata malamar makarantar sakandare mai shekara 29 da haihuwa ce ta zama Tauraruwar gasar ta bana.


Safiyyah Jibril Abubakar ta lashe gasar ne da labarinta mai suna ''Ya Mace'.

Da take bayyana yadda ta ji bayan da ta samu labarin nasarar da ta yi, marubuciyar ta ce, "Lokacin da aka kira ni a waya aka shaida min labarina ya yi nasara, sai na rasa me ma zan ce.

"Sai da na sake duba wayata don na tabbatar ba mafarki nake yi ba, da gaske kira na aka yi aka shaida min na yi nasara."
BBChausa.

No comments:

Post a Comment