Sunday, 28 October 2018

Bidiyon Ganduje: Lauyoyi za su gurfanar da gwamnatin Kano saboda amfani da yara 'yan makaranta

Wasu kungiyar lauyoyi sunyi barazanar shigar da gwamna Abdullahi Ganduje na jihar Kano da Ma'aikatar Ilimi, Hukumar Ilimin Primary na jihar (SUBEB) da Attony Janar, Ibrahim Mukhtar saboda tsoma daliban frimari cikin binciken rashawa da ake gudanarwa kan gwamnan Kano.

Sun kuma bayyana cewa za suyi karar Sakataren Ilimi da Mahukunta na Tarauni da Makarantar Frimari na Musamman ta Unguwa uku saboda amfani da dalibansu cikin harkokin siyasa.

A ranar Alhamis da Jaafar Jaafar ya bayyana gaban majalisar ta jihar Kano domin amsa tambayoyi, an hangi yaran makarantan frimare dauke da kwaleye masu rubutu na goyon bayan gwamna Ganduje suna zanga-zanga a harabar inda majalisar ke zaman sauraron jin ba'asin.

Shugaban kungiyar lauyoyin, Ali Jamilu ya shaidawa Daily Nigerian cewar zanga-zangar abin kunya ce kuma za su yi karar wadda su kayi amfani da yaran a kotu domin ta sabawa sashi na 5(1) na dokar hana bautar da yara na jihar Kano ta 2015.

Hukuncin aikata wannan laifin shine zaman gidan kurkuku na shekara daya ko kuma tara wadda ba tayi kasa da N100,000 ba.
Legit.ng.

No comments:

Post a Comment