Wednesday, 31 October 2018

Buhari bazai samu kuri'a da yawa ba daga Arewa>>Shekarau

Tsohon gwamnan jihar Kano, Malam Ibrahim Shekarau ya bayyana cewa shugaban kasa, Muhammadu Buhari ba zai samu yawan kurin da ya samu a zaben shekarar 2015 ba wannan karin.

Ya bayyana hakane a hirar da yayi da jaridar Daily Trust a gurin wani taron kungiyar masu sayar da magani a Ibadan, da aka tambayeshi akan Buhari da Atiku wa yake ganin zai ci zaben 2019 sai yace, kasancewar Atiku daga Arewa shima ya fito zai sa yawan kuri'un da Buhari zai samu zasu ragu ba kamar shekarar 2015.

Ya kara da cewa amma duk da haka yana kyautata zaton cewa Buharine zai ci zaben amma fa akwai bukatar a tashi tsaye a nemi jama'a.

Da yake magana akan fitarshi daga PDP, Shekarau yace jam'iyyar ta koma hannun Kwankwasone da mutanenshi na kwankwasiyya a jihar kuma zasu yi dana sani a 2019.

No comments:

Post a Comment