Thursday, 25 October 2018

Buhari Ya Shawarci Oshiomhole Ya Sulhunta Da Jigogin APC

Shugaba Muhammad Buhari ya shawarci Shugaban jam'iyyar APC na kasa, Adams Oshiomhole kan ya sulhunta da jigogin jam'iyyar wanda ya hada da wasu gwamnoni wadanda ba su ji dadin yadda Shugaban jam'iyyar ya cire sunayen 'yan takarar da suke marawa baya.


Wata majiya ta tabbatar da cewa, Buhari na kokarin ganin ya maido da zaman lafiya a tsakanin 'ya'yan jam'iyyar don tabbatar da cewa ba a samu baraka ba kafin zaben 2019. Tun bayan zaben fidda gwani na jam'iyyar ne dai, ce ce ku ce ya barke tsakanin wasu gwamnoni da Shugaban jam'iyyar.
Rariya.

No comments:

Post a Comment