Monday, 22 October 2018

Buhari ya yi Allah-wadai da rikicin Kaduna

Shugaban Najeriya Muhammadu Buhari ya yi Allah-wadai da sabon rikicin da ya barke a jihar Kaduna da ke arewa maso yammacin kasar.


Ya ce bai ji dadin yadda rikici ya barke a jihar ba wanda kuma har ya haddasa rasa rayukan mutanen da ba su ji ba su gani ba har 55, kamar yadda ya bayyana a shafinsa na Twitter.

Shugaban Najeriyar, ya ce tuni aka umarci jami'an 'yan sanda da su yi duk abin da ya kamata wajen dawo da zaman lafiya da kwanciyar hankali a sassan jihar.

An dai tura dakarun kwantar da tarzoma na musamman zuwa jihar.

Har ila yau shugaban ya ce rashin mutunta rayuwar dan Adam, abu ne da ba za a amince da shi ba.

Ya ce "rikici ko tashin hankali abu ne marar kyau, don haka ina kira ga shugabannin al'umma da kuma 'yan kasa da ako da yaushe su rinka amfani da tattaunawa da hakuri da kuma juriya domin gujewa tashin hankalin da ka iya janyo babban rikici."

Daga nan ya yaba wa gwamnatin jihar Kaduna saboda matakan gaggawan da ta dauka bayan barkewar rikicin.
BBChausa.

No comments:

Post a Comment