Tuesday, 16 October 2018

Buharine ya lashe zabukan shekarun 2003, 2007 da 2011 amma aka hanashi>>Inji wakilin Amurka a Najeriya

Tsohon wakilin kasar Amurka a Najeriya, John Campbell a wata hira da yayi da gidan talabijin na Channels, an tambayeshi game da batun da ya rubuta a wani littafinshi na cewa shugaba Buharine ya lashe zabukan shekarun 2003, 2007 da 2011 amma duk aka murde aka hanashi.


An tambayeshi ko menene hujjarshi na fadin  haka?

Sai ya kada baki yace yayi magana da mutanen da suka yi aikin zabukan da kuma kungiyoyin sakai na gida Najeriya dana kasashen waje kuma duk sun tabbatar mai da haka, ya kara da cewa, yawancin zaben an murdeshine a lokacin tattara sakamako.

An tambayeshi ko ya samu bayanin haka daga hukumar zabe?

Sai yace a'a.

No comments:

Post a Comment