Wednesday, 17 October 2018

Canada ta halatta sayar da wiwi a shaguna

Kasar Canada ta halasta saida tabar wiwi a shagunan kasar, hakan ya sanya ta zama kasa ta biyu baya ga Uruguay da ta dauki mataki irin haka.


Wannan dai na cikin alkawuran da Firaminista Justin Trudeus ya yi wa 'yan kasar a lokacin yakin neman zabe, wanda ya ce daukar matakin zai rage yawan shan tabar wiwi da ta wuce kima da rage ayyukan ta'addanci.

Wayewar safiyar Laraba lokacin da dokar ta fara aiki, hotunan internet sun nuna yadda mutane suka yi layi a kofar shaguna don sayan tabar wiwi a wasu biranen kasar.

Sai dai ba lallai ne matakin ya yi tasiri a wasu yankuna da gundumomin Canada da suka fitar da na su dokokin haramcin ba.

A yankunan kudanci, manyan shagunan gwamnati ne kadai suke da lasisin sayar da wiwin, a arewaci kuma masu shaguna suke da halaccin.

Gundumomin gabashi baki daya an haramta tu'ammali da ita, saboda kowacce shiyya na da irin na ta tsare-tsare da dokoki a iyakokinta.
BBChausa.

No comments:

Post a Comment