Thursday, 25 October 2018

Daga yanzu duk wanda ya jefo abu daga cikin mota a kan titi zai biya tarar 5000>>Road Safety

Hukumar kula da kiyaye hadura da dokokin kan titi wanda aka fi sani da Road Safety ta bayyana cewa daga yanzu duk wanda aka kama ya jefo abu daga cikin mota yayin da take tafiya a kan titi zai biya tarar naira 5000.


Hukumar reshen jihar Legas ce ta fitar da wannan doka inda tace yadda abu a kan titi yayin da mota ke tafiya mummunar dabi'ace wadda kuma zata iya jawo hadari.

Hukumar ta bayyana hakane ta bakin daya daga cikin ma'aikatanta da ya tattauna da manema labarai, Adedotun Abayomi ya bayyana cewa sun samu korafe-korafe da dama daga gurin masu aikin sharar hanya kamin su dauki wannan mataki.

Ya bukaci masu motocin haya da su karfafawa fasinja amfani da kwandan shara dake cikin mota wajan zubar da kayan datti maimakon jefasu kan titi.

No comments:

Post a Comment