Saturday, 6 October 2018

Dalibin Jami'ar ABU ya kera jirgin yaki, ya saka masa suna 'mai ceton 'yan matan Chibok'

Mun samu labarin wani dalibin Jami'ar Ahmadu Bello da ke Zaria da ya kera jirgin yaki kuma ya sanya mata suna 'Hope For Chibok Girls' waton mai ceton 'yan matan Chibok. Dalibin mai suna Shettima Ali ya kera jirgin ne a bincikensa na kammala digiri.

Wata mai amfani da shafin sada zumunta na Twitter, Ummie Shettima ta ce ta fara wallafa hotunan jirgin da bidiyon yadda dalibin ke nuna yadda jirgin ke tashi inda ta bayyana cewa dalibin jami'ar ABU Zaria ne ya kera.

Abinda ta rubuta: "Dalibin ABU mai karantar Physics, Shettima Ali Kyari ya kera jirgin sama na yaki a matsayin binciken sa na kammala digiri, ya kuma sanya masa suna 'mai ceton 'yan matan Chibok'.
Sunan da dalibin ya sanya wa jirgin ya janyo hankulan mutane da yawa ciki har da mai taimakawa shugaba Muhammadu Buhari a fanin sabuwar kafar yada labarai, Bashir Ahmad.

Ahmad ya yabawa kwazon dalibin a shafinsa na Twitter.
Naija.ng.

No comments:

Post a Comment