Sunday, 7 October 2018

Dalilin da ya sa Buhari bai nada wasu mukamai ba har yanzu?

Fadar shugaban Najeriya ta ce tana jiran majalisar tarayya ta dawo da zamanta domin tura sabbin mukamai da ba a nada ba.


A yayin da yake mayar da martani ga batun sauran nade-naden gwamnatin tarayya da ba a yi ba, Mai magana da yawun shugaban kasa Malam Garba Shehu ya ce wasu makaman sun fi shekaru biyu a gaban majalisar dattijai.

"Mu saurarensu muke yi domin har yanzu ba su gama da su ba," in ji shi.

Har yanzu dai akwai sauran nade-naden mukaman shugabanni da mambobin wasu hukumomin tarayya da gwamnatin ba ta kammala ba.

Wannan kuma na zuwa yayin da ya rage saura kasa da shekara guda wa'adin farko na mulkin gwamnatin Buhari ya kawo karshe.

Masu lura da al'amura na ganin hakan ya saba wa kundin tsarin mulkin kasar, kuma yana kawo cikas ga gudanar da ayyukan hukumomin da abin ya shafa da ma kasa baki daya.

Nasiru Babangida wani mai lura lamurra a Najeriya ya ce ya kamata ace hukumomi kamar hukumar kula da daukar ma'aikata da hukumar raba tattalin arzikin kasa da hukumar INEC an nada wakilai.

Sannan ya ce ya kamata zuwa yanzu an tabbatar da shugabannin hukumomin da ke yaki da rashawa wato EFCC da ICPC da kuma wasu da dama da ba a yi wa wakilai ba.

Masu sharhin dai na ganin wannan na kawo cikas wajen gudanar da ayyukan ma'aikatun na gwamnatin.

Sai dai kuma Malam Garba Shehu ya ce sha'anin nade-nade na hukumomi ba lalle sai a farkon kafa gwamnati ba ko a karshenta ba, ya danganta da lokacin da majalisa ta amince da su.
BBChausa.

No comments:

Post a Comment