Tuesday, 2 October 2018

Dalilin da yasa manyan kasarnan basu so in zama shugaban kasa>>Atiku

Tsohon mataimakin shugaban kasa kuma dan takarar shugaban kasa karkashin jam'iyyar PDP, Atiku Abubakar ya bayyana cewa manyan kasarnan na adawa da shi ne saboda shi ba mutum bane wanda za'a iya juyawa yanda ake so ba.


Atiku yace sun sanshi mutum ne tsayayye wanda ba za'a iya amfani dashi wajan cimma manufa ta wasu tsitrarun mutane ba idan ya zama shugaban kasa.

Yace shiyasa suke ta kokarin bata mai suna ta hanyar kirkirar karya akanshi, yayi kira ga 'yan Najeriya da su kauda kai daga yawan canja jam'iyyun siyasa da yake, maimakon haka su duba yanda ya jajircewa wajan ganin dorewar Najeriya da ci gabanta, kamar yanda Punch ta ruwaito.

Atiku ya kuma bayyana cewa shine yafi kwarewa a cikin 'yan takarar da ke neman tikitin tsayawa shugaban kasa na PDP saboda yayi aiki da gwamnati na tsawon shekaru 20 sannan kuma ya samar da ayyuka ga dubban mutane.

No comments:

Post a Comment