Wednesday, 17 October 2018

Dan Obasanjo ya shiga yiwa Buhari yakin neman zabe

Dan gidan tsohon shugaban kasa, Olusegun Obasanjo me suna, Abraham Olujonwo ya shiga  yiwa shugaban kasa, Muhammadu Buhari yakin neman zaben 2019.


Me taimakawa shugaban kasar ta fannin kafafen sadarwa na zamani, Lauretta Onochie  ce ta bayyana haka ta shafinta na dandalin Twitter inda tace, dan Obasanjo ya shiga yiwa Buhari kamfe.
Dama tun a kwanakin bayane dan Obasanjon ya fito ya gayawa Duniya cewa shi yana tare da Buhari.

No comments:

Post a Comment