Monday, 15 October 2018

Dan Ronaldo ya ci kwallo irin ta babanshi

Tauraron dan kwallon Juventus, Cristiano Ronaldo ya saka bidiyon danshi dake wasa tare da kungiyar kananan yara ta Juve din inda aka ganshi ya ci kwallo, jiya, Lahadi.


Masu iya magana na cewa kyan da ya gaji ubanshi, kusan hakane take shirin kasancewa da dan Ronaldon dan kuwa ya dauko hanyar gadon ubanshi.

Koda a kwanakin baya saida Ronaldon ya bayyanawa 'yan Jarida irin yanda yake fatan dan nashi ya gaje shi.

No comments:

Post a Comment