Thursday, 25 October 2018

Dangote ya zo na 6 cikin musu kudin da suka fi taimakawa mutane a Duniya

Sunan attajirin dan Najeriyarnan Aliko Dangote ya zo a matsayi na 6 cikin mutanen da suka fi taimakawa al'umma a Duniya.

Wata kafar watsa labarai ta kasar Ingila me sun Richtopia ce ta wallafa sunayen masu kudin Duniya da suka fi bayar da taimako ga mutane mabukata jiya, Laraba wanda a ciki ne Dangoten ya zama na 6.

Sunayen masu kudin sune kamar haka:

Warren Buffett

Bill Gates

J. K. Rowlings

Oprah Winfrey

Elon Musk

Aliko Dangote.

Akwai kuma shugaban bankin UBA, Tony Elumelu wanda shima dan Najeriyane yazo na 11 a jerin wanda suka fi bayar da taimakon.

A kwanannan ne Dangoten ya zuba zunzurutun kudi har dala miliyan dubu 1.25 a gidauniyarshi ta Dangote.

Gidauniyar Dangote ce mafi girma ta mutum daya a yankin Afrika ta yamma.

No comments:

Post a Comment