Monday, 15 October 2018

Dattawan Arewa sun bayyana abinda zai sa su zabi Buhari ko Atiku

Da sanadin shafin jaridar The Punch mun samu rahoton cewa, kungiyar dattawan Arewa ta gindaya sharadinta na akida dangane da wanda za ta zaba a yayin babban zabe na 2019 tsakanin shugaban kasa Muhammadu Buhari da kuma Atiku Abubakar.

Kungiyar ta bayyana cewa, baja kolin tsare-tsare, salo da kuma manufofin gudanar da shugabancin Najeriya tsakanin Buhari da tsohon mataimakin shugaban kasa, su za su tantance wanda zai samu goyon bayan ta tsakanin su a yayin babban zabe na 2019.

Shugaban Kungiyar, Alhaji Tanko Yakasai, shine ya bayyana hakan da cewar ba bu wani hanzari na yanke shawarar zaben 2019 a halin yanzu domin kuwa sai sun gamsu da manufofin dan takara kana ya samu goyon bayan kungiyar su.

A sanadiyar haka ya sanya Alhaji Yakasai yake kira ga daukacin al'ummar Najeriya, akan su yi jinkiri na bayyana goyon baya tsakanin Atiku ko Buhari ba tare da sun baja kolin tsare-tsaren su da kuma manufofi na jagorantar kasar nan.
Alhaji Yakasai ya kara da cewa, ba bu dace a halin yanzu al'ummar kasar nan su karbi kowane dan takara ko kuma bayyana goyon baya a gare sa ba tare da ya gabatar da manufofi da kuma shimfidar akidu kan turba ta shugabanci a kasar nan.

A yayin da jam'iyyar APC ta tsayar da shugaba Buhari a matsayin marikin tutar ta yayin zabe na 2019, hakazalika Atiku ya yi nasara ta lashe zaben fidda gwanin takarar kujerar shugaban kasa na jam'iyyar PDP da aka gudanar a makon da shude.
Naija.ng.

No comments:

Post a Comment