Saturday, 20 October 2018

Dokar hana sanya Hijabi da Nikabi ta fara aiki a Aljeriya

Dokar hana sanya Hijabi ko Nikabi a ofisoshi da ma'aikatun gwamnati ta fara aiki a Kasar Aljeriya.

A karkashin hulkuncin an hana saka mayafi, Hijabi ko Nikabi da zai boye surar mutanen da ke aiki a dukkan ofisoshi da ma'aikatun gwamnati.

Firaministan Aljeriya Ahmad Ouyahia ya yi kira ga ma'aikatun gwamnatin kasar da mma ofisoshin gwamnoni kan su kula sosai wajen aiwatar da dokar.

A karon farko a shekarar 2011 ne faransa ta hana sanya Hijabi a ma'aikatun gwamnati.

Majalisar Dokokin Denmark ma ta amince da irin wannan doka a karshen watan Mayu.

A watan Agusta dokar ta fara aiki kuma ana cin tarar wadanda suka ki aiki da ita kudi har Yuro 135.
TRThausa.

No comments:

Post a Comment