Wednesday, 17 October 2018

Dole ka sauka daga mukaminka>>Akpabio ya gayawa Saraki bayan dambarwar da suka sha

Bayan dambarwar hanashi magana da kakakin majalisar dattijai, Bukola Saraki yayi yau, Laraba, Sanata Akpabio ya fito ya gayawa Sarakin cewa yayi shirin sauka daga mukaminnashi.

Akpabion ya shaidawa manema labarai cewa, al'adace ta siyasa a kowane sako na Duniya idan mutum ya canja sheka ya bar jam'iyyar da yake sai ya sauka daga mukaminshi, dan haka Saraki ya kamata cikin girma da arziki ya sauka daga shugabancin majalisar kamar yanda nayi na sauka daga mukamin shugaban marasa rinjaye da na koma APC.
Yace, APC ce mafi rinjaye a majalisar dan haka tana bukatar ta samar da sabon shugabanci.

Da yake sukar PDP yace, shekaru 16 da suka yi suna mulki basu wa yankin kudu maso kudu tsiyar komai ba sai yanzu APC take yin titi daga Akwa-Ibom zuwa Calabar wanda yace a da wannan titin ya zama tarkon mutuwa.


No comments:

Post a Comment