Wednesday, 17 October 2018

Dole mu nemi hakkinmu a Kotu>>Gwamnatin Kano

Gwamnatin Jihar Kano ta ce dole ne ta nemi hakkinta a kotu kan dan jaridar da ya saki hutunan bidiyo da ke nuna gwamna Abdullahi Ganduje na karbar rashawar miliyoyin dala.

Gwamnatin ta ce za ta gurfanar dan jarida Ja'afar Ja'afar a gaban kuliya duk da majalisar jihar ta kafa kwamitin tantance sahihancin hutunan bidiyon da ya saki.

Gwamnatin ta bayyana cewa idan majalisar dokoki za ta iya ladabtar da gwamna, ba ta da hurumin ladabtar da dan jaridar.

Mai bai wa gwamnan na Kano shawara kan harkokin siyasa Alhaji Mustapha Buhari Bakwana ya shaidawa BBC cewa wannan zargi ne da ke da nasaba da zagon-kasa irin na siyasa.

"Abokan adawa ne wadanda ba su bukatar wannan gwamnati da ke yaki da cin hanci da rashawa, shi ne aka fara hada wannan sharrin" in ji shi.

Ya kuma ce don an ga irin yawan kuri'un da gwamna ya ba shugaban kasa a zaben fitar da gwani, shi ya sa aka fara yin zagon-kasa don kada ya samu nasara.

No comments:

Post a Comment