Thursday, 11 October 2018

Dr. Ahmad Gumi da sauran manyan malaman kirista sun jagoranci sasanta Atiku da Obasanjo: Obasanjon yace ya yafe kuma Atikun yafi Buhari

Shehin malamin addinin Islama, Dr. Ahmad Gumi da malamin addinin kirista, Bishop Mattew Hassan Kuka da Bishop David Oyedepo da sauransu ne suka wa tsohon mataimakin shugaban kasa kuma dan takarar shugaban kasa karkashin jam'iyyar PDP, Atiku Abubakar rakiya zuwa gidan Obasanjo.


Rahotannin dake fitowa daga shafin Sahara Reporters da Punch na cewa, a lokacin ganawar tasu, Obasanjo ya taya Atiku murna inda ya kirashi da shugaban kasa me jiran gado.

Obasanjo ya shaidawa manema labarai cewa, ya yafewa Atiku duk wani laifi da yayi mishi saboda shima yana neman gafarar Allah, ya kuma kara da cewa zaben fidda gwanin PDP da Atiku ya lashe ba magudi aka yi ba.

Obasanjo ya kara da cewa, Atikun yafi Shugaba Buhari kwarewa a fannin tattalin Arziki kuma idan ya samu shugabancin Najeriya zai kawo ci gaba sosai ta fannin kasuwanciNo comments:

Post a Comment