Monday, 8 October 2018

Duk da akwai jikakkiya tsakaninsu: Bayan lashe zaben fidda gwanin dan takarar shugaban kasa na PDP, Atiku ya fara zawarcin Obasanjo

Ba boyayyen abu bane rashin jituwar dake tsakanin tsohon shugaban kasa, Olusegun Obasanjo da tsohon mataimakinshi wanda yanzu shine dan takarar shugaban kasa na jam'iyyar PDP, Alhaji Atiku Abubakar.

A kwanakin baya, Obasanjo ya bayyana cewa ba zai taba goyon bayan Atiku akan ko ma wane abu bane, kai idan ma ya goyi bayan Atiku ya san cewa Allah bazai yafe mishi ba. Inda ya kara da cewa duk wani abu da zai durkusar da kasarnan ba zai lamunceshiba.

Shima Atiku yayi wani furuci kwanannan inda yace bashi da matsala da Obasanjo amma idan Obasanjon na da matsala dashi wannan kuma shi ya jiyo.

Saidai a jawabinshi na bayan da aka zabeshi ya zama dan takarar shugaban kasa na jam'iyyar PDP da aka yi a Fatakwal, Atiku ya bayyana cewa ba dan Obasanjo ba da bai zamo abinda ya zamo ba yau.

Ya kara da cewa, zabin da Obasanjo ya mishi a matsayin mataimakin shugaban kasa shine ya bashi damar kawowa inda yake a yanzu, kuma a karkashin tsohon me gidan nashi ya koyi darasi wanda da shine zai yi amfani wajan mulkar Najeriya.

Atiku ya mika godiya ga Obasanjo akan wannan dama da ya bashi.

Saidai abin jira a gani shine ko Obasanjon zai sassauto ya goyi bayan Atikun?

Lokaci dai be bar komai ba.

No comments:

Post a Comment