Sunday, 7 October 2018

Duk da zargin fyade da ake mishi Ronaldo ya ciwa Juve kwallo a karawarsu da Udinese

Zargin da akewa tauraron kwallon kafar Juventus, Cristiano Ronaldo na yi wa wata mata 'yar kasar Amurka Fyade be sa yayi kasa a gwiwa ba wajan yin aikinshi yanda ya kamata ba dan kuwa a wasan da Juve ta buga jiya, Asabar da Udinese, Ronaldon ya ci kwallo.


Ronaldo ya ciwa Juve kwallo ta biyu wadda ta kaita ga samun nasara a wasan da ci 2-0.

A lokacin da ya shiga filin wasan, masoya kwallon kafa sun rika kiran sunanshi ana hargowa.

No comments:

Post a Comment