Thursday, 11 October 2018

Duk Duniyarnan babu macen da zata fahimceni>>Adam A. Zango

Tauraron fina-finan Hausa kuma mawaki, Adam A. Zango ya yi wani rubutu a dandalinshi na sada zumunta da ya dauki hankulan abokan aiki da masoyanshi.


Abinda Adamun ya rubuta shine, Gaskiya duk Duniyarnan babu macen da zata fahimceni.

A watan daya gabatane mujallar Fim ta wallafa labarin cewa, Adamun ya saki matarshi, labarin da shima ya jawo cece-kuce sosai akan Adamun.

Saidai kwanaki kadan bayan wancan labarin na mujallar fim, Adamu ya wallafa a shafinshi cewa ya saiwa matarshi sabuwar mota, hakan ya saka wasu masoyanshi cikin rudani da tunanin kodai wancan labari na Mujallar fim ba gaskiya bane?

Wani abu dai da za'a iya lura dashi shine tunda labarin sakin matar tashi ya watsu, ba'a sake ganin Adamun ya wallafa hotonta a dandalinshi na sada zumunta ba.

Yanzu dai wannan magana da yayi tasa da dama daga cikin masoya da wasu daga cikin abokan aikinshi suka rika bashi baki da cewa bai kamata ya rika fadin irin wannan magana ba.

Koma dai menene sai muce komai yayi zafi maganinshi Allah.

No comments:

Post a Comment