Monday, 1 October 2018

Fadakarwa akan hankali da mugayen kawaye>>Daga Angry Ustaz

Tauraron me fadakarwa a shafin Twitter, Mustafa wanda aka fi sani da Angry Ustaz yayi kira ga mata masu bin kawayen banza da su hankalta su kula daina.


Ya fadi kalaman da kawayen banzan ke amfani dasu wajan jan hankalin 'yan mata kamar haka:

Zo na hadaki da wani Senator.
Zo na kaiki wajan wani Alhaji.
Zo yarinya a canza maki rayuwa.
Zo, zo, zo.
Haka zata rika janki har sai ta kaiki ga halaka.
Su alhazawan a banza suke kyauta?
Karki maida kanki karuwa sabida abin Duniya.
Kiyi hankali da mugayen kawaye.
A tuba.

No comments:

Post a Comment