Tuesday, 23 October 2018

Faidar yin aboki na gari>>Malam Aminu Ibrahim Daurawa

Idan za kayi abota kayi da masu hankali
Domin 
idan baka nan zasu kare mutunci ka. 
Idan  basu ganka ba zasu nemeka. 
Idan ka samu zasu tayaka murna. 
Idan kayi kuskure zasu gyara maka. 

Idan za suyi addu'a ba zasu  manta da kai ba. 
Idan baka da lafiya zasu duba ka suyi maka addu'a. 
Idan zaa cuce ka zasu taimake ka.
Idan ka mutu zasu yi maka addua, kuma su taimaki iyalanka a bayanka.
Wanda ya rasa abokai na gari yayi asara
Allah ka bamu abokai na gari.

No comments:

Post a Comment