Saturday, 6 October 2018

Fari sun yi sanadiyyar mutuwar mutane 100 a Kongo

Bulluwar wata cuta a kasar Jamhuriyyar Demokradiyyar Kongo ta yi sanadiyar mutuwar mutane 100.


Komishinan lafiyar jihar Kwango Jean-Gauthier Kibangu, ya bayyana cewar wasu mutane a garin Kahemba da suka shiga gandun daji domin kamun farin matafila sun dawo suna amai da gudawa tare da kuma ciwon kai da ciki.

A cikin makonni uku lamarin ya yi sanadiyar mutuwar mutane ɗari, kawo yanzu dai ba'a gano nau'in cutar ba, tuni dai an fara bincike akan lamarin a babban birnin kasar Kinshasa.

Mai magana da yawun wata kungiya mai zaman kanta Guiscard Gibembe a garin Kahemba ya bayyana cewar fari sun kasance ɗaya daga cikin muhimman abincin mutanen yankin.

A watan Yuli an samu bulluwar wata cuta mai suna Konzo ga mutane 200 a ƙasar.

Wannan cutar dake sanya kumburin ƙafa da makamantansu nada nasaba da cin rogo da sauran kayyayakin marmari ba tare da an wanke ba.
TRThausa.

No comments:

Post a Comment