Thursday, 4 October 2018

GA HANYA MAFI SAUKI DA ZA'ABI A GANO WADANDA SUKA HALLAKA JANAR IDRIS ALKALI


Muna kira ga rundinar sojin Nigeria karkashin jagorancin shugaba mai adalci Laftanar Janar Tukar Yusuf Buratai (HafizahulLah) da ayi amfani da wannan shawara na bincike da zan bayar, a nutsu sosai a karanci wannan shawaran da zan bayar


Abu na farko: Tunda har an samu nasaran gano motar Janar Idris Alkali a cikin kududdufi a kauyen Dura-Du, kuma rundinar sojin Nigeria tace wannan itace nambar wayan Janar Idris Alkali 09056890335 wanda matarshi Hajiya Salamat tace ta kirashi da nambar yace mata ya iso Jos, to abinda ya kamata ayi shine, aje ofishin Glo Masts ko MTN Mast ko Airtel Masts, wato ina nufin Masts na kamfanin layin da shi Janar Idris Alkali yake amfani dashi, kuma Masts din da yake bada service a wannan kauye na Dura-Du 

Idan anje wajen Mast din da yake bada Service a wannan garin na Dura-Du, sai a duba a ranar da Janar Idris Alkali ya bace nambar wayoyi nawa suka shiga cikin ma'adanar bayanai na Masts din garin wanda shi wannan Mast din ya basu Service?. Na farko kenan!

Abu na biyu: sai a duba a gani kamar karfe nawa Janar Idris Alkali ya shiga garin? Misali daga karfe 12 na rana zuwa karfe 1 na rana ya isa garin Dura-Du akayi garkuwa dashi, sai a duba bayanan service wanda Mast na layin wayarshi ya bayar za'aga nambar wayoyin dukkan wadanda sukaje kusa da nambar wayan Janar Idris Alkali ko sun kai mutum sama da dubu daya, indai layin wayarsu iri dayane da na Janar Idris zai nuna, domin a binciken da mukayi wayar Janar Idris Alkali bai 6ata ba tun ranar 3-9-2018 har zuwa 12-9-2018 kafin cajin wayarshi ya kare

Abu na uku: Za'a iya yin bincike a gano wayar Janar Idris Alkali yana wani guri ne, sannan a gano ga wayoyin da suka wuce ta kusa da wayarshi, zai bada thesame loaction dauke da layukan waya irin na Janar Idris Alkali ko sun kai dubu mutukar sunje kusa da wayarshi, duka za'a iya yin bincike a gano ta dalilin Mast da yake bada service a kauyen Dura- Du

Abu na hudu: Matukar akabi wadannan matakai da na zayyana wallahi na rantse da girman Allah Ubangijin Musulunci da Musulmai za'a gano wadanda sukayi garkuwa da Janar Idris Alkali suka kasheshi, bincike ba karya bane, Allah (SWT) Bai taba kunyata masu gudanar da bincike na gaskiya kuma akan gaskiya ba, idan ma anyi musayen bayanan sirri tsakanin makasan da wadanda suka dinga bin diddigin tafiyar da Janar Idris yayi tun daga Abuja har zuwa wannan garin na Dura-Du suna kiran waya suna bada bayanan sirri duka za'a ganosu cikin sauki har ma da hotunansu

Ina mai tabbatar muku idan kwararren Police Intelligence kuma Investigator ne yana zuwa gurin binciken kisan Janar Idris Alkali indai yasan me yakeyi to wannan shine matakin da zaibi, komai yawan wadanda sukaje kusa da Janar Idris Alkali za'a ganosu ta dalilin Masts na layin wayarsa da kuma nasu wayoyin, shi wannan Masts din kamar tsarin mahadar rediyo wato frequency haka yake, yake tattara dukkan bayananshi ya adana, ana zuwa binciken Masts din za'a tabi bayanan abinda ya adana na ranar 3-9-2018

Kuma har yanzu ba'a makara ba, karku rena bincikenmu, ku assasa kubi wannan tsarin da na bayar zakusha mamaki, da taimakon Allah za'a kama wadanda suke dauke da alhakkin zubar da jinin Janar Idris Alkali da duk wadanda suke da hannu a ciki, ba zasu taba tsira ba duk inda suke a Nigeria matukar akabi wannan mataki na bincike

Muna rokon Allah Ya sa wannan sako na Datti Assalafiy zai kai inda ya dace Amin
Allah Ka jikan Jan Gwarzo Janar Idris Muhammad Alkali, Allah Ka sa ya dace da mutiwar shahada, sannan ka tona asirin wadanda suke dauke da alhakkin salwantar da rayuwarshi Amin.

No comments:

Post a Comment