Wednesday, 24 October 2018

Ganduje ya lashe wata gagaruman kyauta da ta gagari sauran gwamnoni

Wata cibiya mai suna LEAD Innovation da ke Jihar Legas ta karrama Gwamna Dr. Abdullahi Ganduje na Jihar Kano da lambar yabo na gwamna da ya fi bajinta a fannin samar da ayyukan inganta rayuwan al'umma a duk Najeriya.


An mika wa Ganduje lambar yabon ne a ranar Lahadi 10 ga watan Oktoba a wata liyafa da LEAD Innovation ta shirya a Oriental Hotel da ke Victoria Island a Legas.

Gwamnan ya mika godiyarsa ga cibiyar da ta shirya taron da kuma karrama shi da ta yi.

Ganduje ya kuma yi amfani da damar domin bayyana wasu nasarori da gwamnatinsa ta samu a cikin shekaru uku da suka wuce: "Mun samu gagarumin nasara wajen kaddamar da shirye-shiryen mu na cigaba domin tabbatar da cewa mutanen Kano sun amfani romon canji.

"Baya ga haka, mun tabbatar da cewar mun watsa ayyukan a dukkan sassan jihar a fanin gine-gine kama aikin gina tituna da gyaransu, gine ginen makarantu da asibitoci, samar da ruwan sha, kiyaye muhalli, noma, tattalin arzikin da sauransu."

Duk dai a cikin jawabinsa, gwamnan ya ce taken taron na wannan shekarar ya nuna cewar wadanda suka shirya taron sun mayar da hankali wajen binciko mutane masu baiwa da sana'o'i a nahiyar Afirka domin kara musu kwarin gwiwa.
Legit.ng.

No comments:

Post a Comment