Thursday, 25 October 2018

Ganduje ya tanadi ‘yan daba 3000 dan su farwa Jaafar Jaafar

Gwamnatin jihar Kano karkashin Ganduje ya tanadi ‘Yan daba kimanin 3000 dan su farwa mawallafin wannan jarida ta Daily Nigerian Malam Jaafar Jaafar a yayin da aka shirya shiryen da ake yi na sauraren bahasin Jaafar Jaafar kan rahoton faifan bidiyon da ya wallafa aka nuna Gwamnan Kano Ganduje na karbar cin hanci na Dakar Amurka.


Tun bayan fitar wannan faifan bidiyo ne dai majalisar dokokin jihar Kano ta kafa wani kwamati mai mutum bakwai karkashin jagorancin Baffa Babba Danagundi domin kwamitin yayi bincike ya gano gaskiyar lamarin.

A yayin gudanar da aikin kwamitin, an gayyaci Mawallafin jaridar Malam Jaafar Jaafar domin ya bayyana a gaban kwamatin don bayan da shaida kan sahihancin faifan bidiyon da ya wallafa.

Saidai wasu bayanai na asiri sun tabbatar da cewar Gwamnatin jihar Kano karkashin Abdullahi Umar Ganduje ya tanadi ‘Yan daba kimanin 3000 daga kananan hukumomin jihar Kano 44 domin su zo su tayar da yamutsi a lokacin da ake aikin kwamitin, abinda zai sabbaba musu farwa Jaafar Jaafar.
Daily Nigerian Hausa.

No comments:

Post a Comment