Wednesday, 24 October 2018

Gasar Zakarun Turai: Juventus ta doke Man Utd a gida da ci 1-0

Kungiyar Juventus ta doke Manchester United da ci 1 - 0 a Old Trafford.


Kwallon da Paulo Dybala na kungiyar Juventus ya jefa a ragar Juventus kafin a tafi hutun rabin lokaci ce ta raba kungiyoyin biyu.

Haka aka buga wasan, wanda tsohon dan wasan United Cristiano Ronaldo ya buga wa kungiyar ta Juventus, wanda shi ne dawowarsa ta farko zuwa Old Trafford tun da ya koma kungiyar a bana.

United za su tafi birnin Turin domin karawa a karo na biyu da Juventus ranar 7 ga watan Nuwamba.
BBChausa.

No comments:

Post a Comment