Sunday, 28 October 2018

Gaskiyar zance a kan takardun Buhari

Batun rashin mika takardun shugaba Buhari ga hukumar zabe mai zaman kanta na cigaba da jawo cece-kuce a tsakanin 'yan Najeriya, musamman bangaren 'yan jam'iyyar adawa ta PDP.


Ko a shekarar 2015 sai da batun takardun karatun Buhari su ka haifar da irin wadannan maganganu, amma hakan bai hana shi yin takara ba duk da kasancewar yana jam'iyyar adawa ne a wancan lokacin.

Wani nazari da tuntuba da jaridar Legit.ng ta yi ya bayyana muhimmanc abubuwa 5 da ya kamata jama'a su sani a kan tsarin karatun gidan soja.

1. Daga lokacin da mutum zai shiga gidan soja dole ne ya ba su takardun karatunsa na asali (original)

2. Duk takardun da mutum ya bayar za a saka su cikin fayil dinsa a ajiye.

3. Takardun karatun ma fi yawan tsofin sojojin kasar nan sun bata a gidan soja

4. Batan takardun na da alaka da sakaci irin na hukumomin Najeriya, musamman wajen adana bayanai.

5. Yin takardar kotu (Affidavit) ya isa zama hujja ga duk tsohon sojan da takardunsa su ka bata
Legit.ng.


No comments:

Post a Comment