Saturday, 6 October 2018

Gayyatar 'yan sanda: Duk cikin wanda suka yi zanga-zanga mu kadai kuka gani>>Dino Melaye ga 'yansanda

Bayan zanga-zangar da 'yan PDP suka yi jiya a Abuja ta nuna kin amincewa da sakamakon zaben jihar Osun inda suke zargin APC da yin murdiya, zanga-zangar ta kare da rikici tsakanin su da 'yansanda wanda hakan yasa hukumar 'yansandan ta bukaci nan da ranar Litinin kakakin majlisar dattijai, Bukola Saraki da Sanata Dino Melaye da Sanata Ben Bruce da su bayyana gabanta dan amsa tambayoyi.



Sanarwar tace anga wadannan sanatoci a kyamara suna cin zarafin 'yansanda sannan kuma sun tare hanya suka takurawa jama'a.

Da yake mayar da martani akan wannan sanarwa, Sanata Dino Melaye yace, watau duk cikin wadanda suka yi zanga-zanga Saraki da Melaye da Murray Bruce kawai aka gani a kyamara.

No comments:

Post a Comment