Monday, 15 October 2018

Gwamna Ganduje ya je rangadi wajan aikin gadar Sabon Gari

Wadannan kayatattun hotuna gadar sabon Gari ce dake Kano da ake kan ginawa, gwamnan jihar, Dr. Abdullahi Umar Ganduje ya je rangadi gurin aikin a yau, kamar yanda me taimaka mishi ta fannin kafafen sadarwa, Salihu Tanko Yakasai ya bayyana.


Gwamnatin Ganduje ta gaji wannan aikine daga gwamnatin Kwankwaso yayin da aikin ke matakin kashi 30 na kammalawa, zuwa watan gobe idan Allah ya yadda za'a kammala aikin wannan gada.No comments:

Post a Comment