Wednesday, 3 October 2018

Gwamnan jihar Borno Kashim Shattima ya fashe dakuka a gaban jama'a

A gurin zaben fidda gwanin dan takarar gwamna na jihar Borno a karkashin jam'iyyar APC an ga gwamnan jihar me barin gado, Kashim Shattima ya fashe da kuka a gaban jama'a saboda shaukin abinda ya wakana a gurin.


Gwamnan ya zabi farfesa Babagana Zulum a matsayin dan takararshi yayin da abokin hamayyarshi, Barista Kaka Shehu Lawan ya janye mai ya kuma goyi bayanshi sannan yayi kira ga masoyanshi da su zabi Zulum.

Zulum dai shine ya lashe zaben a tsakanin 'yan takara 21 da suka nemi tikitin.No comments:

Post a Comment