Wednesday, 3 October 2018

Gwamnan Legas ya fadi zaben fidda gwani na APC

Jam'iyyar APC reshen jihar Legas ta sanar da cewar Babajide Sanwo-Olu ne wanda ya yi nasara a zaben fidda gwani na takarar kujerar gwamna a jihar a zaben 2019.


Ciyaman din jam'iyyar, Tunde Balogun ne ya bayar da sanarwan ranar Talata, 2 ga watan Oktoba a Sakatariyar jam'iyyar da ke Legas.

A cewarsa, Sanwo - Olu ya samu kuri'u 970,851 yayin da gwamni mai ci yanzu, Akinwunmi Ambode ya samu kuri'u 72,901 a zaben.

Wannan sanarwar tana zuwa ne bayan kwamitin gudanarwa na kasa na jam'iyyar ta soke zaben da aka gudanar.

Dama dai Asiwaju Bola Tinubu yace gwamna Ambode ya yi bajinta a matsayinsa na gwamna amma baya tafiya tare da 'yan jam'iyya.

Ana ganin wannan dalilin ne yasa Asiwaju Bola Tinubu ya juyawa Akinwunmi Ambode baya a yunkurinsa na yin tazarce a jihar. Tinubu ya bayyana a fili cewar yana goyon bayan Babajide Sanwo-Olu ne wadda galibin 'yan majalisar jihar suma sun mara masa baya.
Naija.ng.

No comments:

Post a Comment