Wednesday, 24 October 2018

Gwamnati na shirin kayyade yawan 'ya'yan da mata zasu rika haihuwa

Gwamnatin tarayya ta bayyana cewa tana shirye-shiryen fito da tsarin kayyade yawan 'ya'yan da mata zasu rika haihuwa a kasarnan.


Maganar ta fito ne daga bakin ministar kudi, Zainab Ahmed inda ta bayyana cewa gwamnatin ta saka shugabannin al'umma na gargajiya a cikin wannan tsari nata dan ya samu karbuwa ga mutane,kamar yanda jaridar Punch ta ruwaito.

Zainab ta yi wannan maganane a ganawar da tayi da 'yan jarida jiya a gurin wani taron ci gaban tattalin arzikin Najeriya da ya faru a Abuja.

Ta bayyana cewa, yawan haihuwa barkatai na daga cikin abinda ke kawowa tsarin habbaka tattalin arziki da kuma ci gaban al'umma da suka sa a gaba cikas, shiyasa suke so su kawar da matsalar.

No comments:

Post a Comment