Tuesday, 9 October 2018

Gwamnatin Adamawa ta juyawa Atiku baya ta rungumi Buhari: Fayose yayi barazanar ficewa daga PDP saboda nasarar Atiku

Gwamna Jibrilla Bindow na jihar Adamawa, mahaifar dan takarar shugaban kasa karkashin jam'iyyar PDP, Alhaji Atiku Abubakar ya juya mishi baya inda ya rungumi shugaba Buhari a matsayin dan takararshi na shugaban kasa a zaben 2019 me zuwa.

Gwamnan ta hannun kwamishinan watsa labarai na jihar, Sajoh Ahmed ya nesanta kanshi daga wani yunkurin bata suna da wasu ke shirinyi inda ake buga fastarshi da ta wani dan takarar shugaban kasa bana APC ba.

Sanarwar tace gwamna Bindow dan APC ne kuma be da wani dan takarar shugaban kasa da zai goyawa baya da ya wuce shugaban kasa, Muhammadu Buhari domin abubuwan ci gaba da ya kawowa jihar a bayyane suke.

Sannan yayi kiran cewa duk wata fasta da za'a gani wadda ba shi da Buhari ba to mutane su yi watsi da ita, kamar yanda jaridar The Nation ta ruwaito.

Shi kuma gwannan jihar Ekiti me barin gado, Ayodele Fayose barazanar barin jam'iyyar PDP yayi bayan da Atiku ya lashe zaben fidda gwanin takarar shugaban kasa na jam'iyyar.

A wata sanarwa da ya fitar ya bayyana cewa, be yi nadamar hada kai da gwamnan jihar Rivers, Wike ba wajan goyon bayan gwamnan jihar Sakkwato, Aminu Waziri Tambuwal akan lashe zaben fidda gwanin jam'iyyar ba.

Kuma yana so yayi tuni akan cewa sune fa suka tsaya tsayin daka suka rike jam'iyyar bayan da sauran mazan jam'iyyar suka zama mata amma yanzu wasu suna nuna cewa wai zasu iya yi su kadai, to zasu zuba ido su ga iya gudun ruwansu.

Fayose yace zai ma fa iya ficewa daga jam'iyyar idan abubuwa suka yi kamari.

Amma yace ya yaba da shiga tsanin da wasu manya su ka yi akan wannan magana kuma har yanzu yana nan yana tuntuba akan matakin da zai dauka nan gaba.

No comments:

Post a Comment