Friday, 26 October 2018

Gwamnatin Jihar Kaduna ta sake sanya dokar hana zirga zirga na awa 24

Gwamnatin Jihar Kaduna ta sake sanya dokar hana zirga zirga a garin Kaduna da Kasuwan Magani da Kajuru da Ketari da kuma Kachia. Wannan dokar ta fara yanzu ne har zuwa yadda hali ya yi. 


Gwamnati ta dauki wannan matakin ne don a kara samun zaman lafiya a jihar a lokacin da al’umma ke juyayin rashin Agom Adara wanda aka samu wasu ‘yan ta’adda suka kashe shi da safiyar yau bayan sun yi garkuwa da shi tun a makon jiya. 

Don haka ana kira ga al’ummar Jihar Kaduna su zauna lafiya kada su yarda wadanda suka yi wannan ta’addanci su yi amfani da wannan dama don raba kawunan al’umma. 

Allah ya zaunar da Jihar Kaduna lafiya 
Allah ya zaunar da kasarmu Nijeriya lafiya

No comments:

Post a Comment