Sunday, 28 October 2018

Gwamnatin tarayya ta bayyana yanda zata fitar da miliyoyin 'yan Najeriya daga kangin talauci

A yayin da zaben shekarar 2019 ke kara matsowa, 'yan siyasa na ta bayyana alkawuran ayyukan da zasu yiwa 'yan Najeriya idan suka zabesu, wani bawan Allah ya tabo maganar talauci inda yace mutanen Najeriya sun fi fama da talauci lokacin mulkin Jonathan fiye da lokacin mulkin Buhari.


Ya bayar da hujjar cewa, a shekarar 2012 mutane miliyan 100 ne ke fama da talauci a Najeriya amma Najeriya bata zama matattarar talaucin Duniya ba.

Yace amma a shekarar 2018 mutane miliyan 87 ke fama da talauci a Najeriya amma Najeriyar ta zama matattarar talaucin Duniya.

Wannan magana tashi dai kamar shagubene.

Me baiwa shugaban kasa shawara ta fannin sabbin kafafen sadarwa, Bashir Ahmad ya mayar da martani inda ya bayyana tsare-tsaren da gwamnatin Buharin ta bullo da su dan fitar da mutanen Najeriyar daga kangin talauci.

Yace bashin da shugaban kasa Buhari ke bayarwa, da baiwa marasa galihu tallafin kudi da kuma ciyar da 'yan makaranta da N-Power, da tallafin kudin dubu 10 da ake baiwa masu kananan sana'o'i da dai suransu zai taimaka wajan fitar da miliyoyin 'yan Najeriya daga talauci.


No comments:

Post a Comment