Thursday, 18 October 2018

Gwamnatin Tarayya Ta Kammala Aikin Samar Da Katafaren Cibiyar Wutar Lantarki A Jihar Kano

Gwamnatin tarayya karkashin jagorancin shugaban kasa Muhammadu Buhari ta yi nasarar kammala aikin samar da cibiyar wutar lantarki mai karfin 30/40MVA 132/33kV' a garin Wudil dake jihar Kano.


A ziyarar gani da ido da cibiyar kafar yada labarai ta shugaba Buhari (The Buhari New Media Centre) ta kai wurin aikin a jiya Laraba karkashin jagorancin Hadimin Shugaban Kasa, Bashir Ahmad, wanda zai kara karfin wutar lantarki ga cibiyar samar da wuta ta jihar Kano, aikin zai fadada samar da wuta a kananan hukumomin Gaya, Takai, Garko Wudil da sauransu.

Wadannan garuruwa wadanda suna daga cikin kwastomomin cibiyar samar da wutar lantarki ta jihar Kano, ana sa ran za su samu karin wadatar wuta.
Rariya.

No comments:

Post a Comment