Sunday, 28 October 2018

GWANI NA DUDU: ME KA SANI GAME DA ALKUR'ANIN DA Jaafar Jaafar YA JE DA SHI KANO

Gwani na dudu wani mutum ne makarancin alqur'ani kuma hafizi Gangaran me gudun duniya da akayi shi acikin birnin kano unguwar koki, sunansa na gaskiya Ibrahim, yana da mata guda biyu masu suna iri daya dudu da dudu, Wanda Dukkaninsu mahaddatan alqur'ani ne.


Yayi yawon Neman ilimin addinin muslinci musan man ilimin alqur'ani da tajwidi da Tafsiri, Dan ana cewa har kasashen larabawa yashiga Dan Neman ilimin Qur'ani. Duk da lokacin ba mota a kafa ya dinga tafiya.

Makarantarsa itace babbar tsangaya wacce Duk wani me asali a alqur'ani a birnin Kano tarihinsa yake komawa gareta.
Ga kadan daga cikin almajiransa: 

1_Gwani Rabiu Dan Tunki. ( mahaifin khalifa isyaka Rabiu
2_ Alhaji Alhassan Dan tata.
3_ Gwani Salihu Dan zarga ( mahaifin Gwani yahuza)
4_ Gwani Salihu Dan turaki ( mahaifin Gwani Aliyu limamin koki) Wanda shine kakana.
5- Gwani Abubakar turaki( malam Turaki) kakansu GWANI Lawi da Gwani Muntaqa.
ME AKE NUFI DA QUR'ANI BUGUN GWANI NA DUDU.

Gwani na dudu yakasance yana rubuta Qur'ani da hannu, sabo da lokacin bature be kawo na'ura wacce ake buga alqur'ani da ita ba,
mutanen lokacinsa suna dauka babu wani alqur'ani me daraja da za'ai rantsuwa dashi idan ba Wanda Gwani na dudu yarubuta ba.
a yanzu Gwani na dudu yakai kusan shekara 70 da rasuwa, amma har yanzu ana karatu a inda ya kafa makarantarsa tun wancen lokacin..

Gwani na dudu yana da Yaya da jikoki mahaddatan alqur'ani fiye da dubu.

Wanda yafi shahara a yanzu acikin su shine Gwani yahuza Gwani Dan zarga babban Alqalin musabaqar alqur'ani na Africa.
Gwani Lawi shugaban mahaddatan alqur'ani na Nigeria.

Addu'ar da mukeyi ko yaushe, Ya Allah yanda mutanan nan su ka yi wa Qur'ani hidima Allah Ka kula da bayansu.
Maje El-Hajeej Hotoro.

No comments:

Post a Comment