Friday, 5 October 2018

Har yanzu Shehu Sanine dan takarar Kaduna ta tsakiya>>APC

A yayin da rahotannin dake fitowa daga jihar kaduna ke cewa jam'iyyar APC ta janye tikitin da ta baiwa sanata Shehu Sani a matsayin dan takara da ya tilo da zai yi takarar Kaduna ta tsakiya inda har abokin hamayyarshi wanda kuma ake wa kallon shine gwamnan jihar El-Rufai ke goyawa baya, Uba Sani ya fito ya ce jam'iyyar ta tantanceshi kuma ta yadda ayi zabe.


Jaridar Premium times tace ta samu daga majiya me karfi ta gidan gwamnan cewa shugaban APC ya aikewa da gwamna El-Rufai sakon cewa yayi hakuri akan abinda ya faru za'a gudanar da zabe.

Saidai kuma me magana da yawun jam'iyyar APC na kasa, Yekini Nabina ya bayyanawa jaridar cewa har yanzu sanata Shehu Sanine dan takara daya tilo da suka sani da zai yi takarar kujerar Sanatan.

Gwamna El-Rufai dai da Sanata Shehu Sani basa ga maciji inda suka sha sukar juna da miyagun kalamai.

No comments:

Post a Comment