Wednesday, 3 October 2018

Hotunan yanda girgizar kasa tayi barna a kasar Indonesia

A ranar Juma'ar data gabata ne aka samu girgizar kasa da karfin ya kai 7.5 a ma'aunin kimiyya wanda sanadiyyar haka aka samu tsunami ateku ya tumbatsa ya shiga garin Peru da karfi ya kuma yi sanadin asarar Dukiyoyi da rayuka.


Masana a kasar sun fitar da kiyasin cewa mutane sama da 1200 ne suka rasa rayukansu kuma ana sa ran yawan wanda suka mutu din zai karu dan ana ci gaba da tonowa da kuma binciken gine-gine da suka ruguje dan zakulo gawarwaki.

Mutanen da suka rasa 'yan uwansu a wannan iftila'i sun rika ziyartar inda aka ajiye gawarwaki dan ganin ko zasu ga na 'yan uwansu.

An rika yiwa mutane kabarin gama gari na kimanin gawarwaki dubu a lokaci guda ana binne su.
A wadannan hotunan na kasa, wata matace ake kokarin cetowa daga inda ta makale.

An samu masallatai, motoci, tituna da gadoji da suka lalace sanadiyyar wannan girgizar kasa. Wasu mutane sun haye saman rufin gidajensu dan gujewa ambaliyar.Akwai tsuburai da yawa a kasar Indonesia, bayan faruwar girgizar kasar, gwamnati ta tura babban jirgin ceto na soji dan su dauko mutanen da suka makale sannan kuma an raba musu kayan agaji.

Wasu kuwa a yayin da ake fama da wannan ibtila'i sun yi amfani da wannan dama wajan satar kaya a manya-manyan shagunan garin da girgizar kasar ta lalata.

Wani mutum hadda satar talabijin, wasu kuwa kayan abinci dadai sauransu.

An sake samun rahoton wata girgizar kasar wadda bata yi karfi ba sosai a Indonesian da kuma aman wuta da duwatsu suka fara yi yayin da ake tsaka da jimamin wadda ta faru ranar Juma'a.
No comments:

Post a Comment