Friday, 5 October 2018

Hukumar 'yansanda ta gayyaci Saraki, Dino Melaye da Ben Bruce akan zanga-zanga

Hukumar 'yansandan Najeriya ta gayyaci kakakin majalisar dattawa, Bukola Saraki da Sanata Dino Melaye da Sanata Ben Bruce da su bayyana a gabansu ranar Litinin me zuwa saboda zanga-zangar da sukayi yau a Abuja da suka tare hanyar Shehu Shagari dake gaban hedikwatar 'yansandan suka takurawa jama'a.


Sanarwar kamar yanda Vanguard ta ruwaito na cewa, akwai kuma cin mutuncin 'yansanda da Sanatocin suka yi inda suka rika turesu suna dukansu dan shiga farfajiyar Hedikwatar da karfin tsiya.

Sanarwar ta kuma ce, 'yansandan dake bakin aikin kare Hedikwatar tasu sun yi amfani da karfi na daidai misali wajan tarwatsa masu zanga-zangar.

'Yan PDP din dai sun yi wannan zanga-zangane dan nuna kin amincewa da sakamakon zaben jihar Osun inda suka ce jam'iyya me mulki APC ta murde zaben, kamin ziyartar hedikwatar 'yansanda, 'yan PDP din sun kuma ziyarci hukumar zabe ta kasa, INEC dan isar da kokensu.


No comments:

Post a Comment