Tuesday, 9 October 2018

Idan Atiku ya zama shugaban kasa kashin Najeriya ya bushe: Fadar shugaban kasa ta bayyana yawan kudin da Atikun ya bayar cin hanci wajan zaben fidda gwani

Fadar shugaban kasa ta hannun me taimakawa shugaban akan shafukan sada zumunta, Lauretta Onochie ta bayyana makudan kudin da Atiku Abubakar ya rabawa 'yan jam'iyyar PDP da har suka yadda suka zabeshi dan takarar su da kuma me zai faru ga 'yan Najeriya idan ya zama shugaban kasa.

A wani sako da ta fitar ta dandalinta na Twitter, Lauretta Onochie tace idan mutumin da ya bayar da cin hancin miliyan dubu 42 ga wakilan jam'iyya ya zama shugaban kasa,watau Atiku, to kashin 'yan Najeriya ya bushe.

Ta karasa da cewa amma Alhamdulillahi 'yan Najeriyar nada wayau.

No comments:

Post a Comment