Monday, 8 October 2018

'Idan da Bush Buhari zai tsaya takara to wallahi Bush zan zaba'

A yayin da babban zaben shekarar 2019 ke kara matsowa, 'yan Najeriya na ta bayyana mabanbanta ra'ayoyinsu akan 'yan siyasar da zasu zaba da wanda ba zasu zaba ba, daya daga cikin masu shirya fina-finan Hausa da kuma me bayar da umarni suma sun bayyana nasu ra'ayin akan zaben shugaba Buhari.


Me shirya fim din Hausa, Shazali Kamfa ya bayyana cewa, wallahi ko da George Bush Buhari zai tsaya takara wallahi George Bush zan zaba.

Da yake bayyana ra'ayinshi akan akan wannan magana me bayar da umarni, Aminu S. Bono shima yace, wallahi wallahi nima haka in yaso masu bada aljanna kada su bamu saboda bamu zabi Buhari ba.

No comments:

Post a Comment