Saturday, 13 October 2018

Ina da bidiyon Ganduje yana karbar cin hanci zan kuma sake su>>Jaafar Jaafar

A hirarsa da BBC, Jaafar Jaafar, ya ce baya tsoron shari'a domin ya na da hujojji masu karfi da ya dogara da su kafin wallafa wannan labarin.


Dan jaridar ya ce, ya samu hotunan bidiyo sama da goma sha biyar da ke nuna yadda gwamnan ke karbar na goro daga hannu 'yan kwangila.

Kwararru sun yi bincike a kan bidiyon, sannan kuma sun tabbatar da sahihancinsa ba bu batun sharri ko kage ko kuma siddabarun harkar komfuta, inji Jaafar.

'Nan da dan wani lokaci kadan zan fitar da bidiyon kuma abin da ya sa aka samu tsaiko, so nake na ga na samu wuri na zauna lafiya tare da iyali na''.

Tuni dai gwamnatin jihar Kano ta yi watsi da zarge-zargen da ke cikin wannan labari, inda ta ce ana yunkurin bata wa gwamnan jihar suna ne kawai.

No comments:

Post a Comment