Wednesday, 3 October 2018

Ina so na wuce bajintar Messi>> Kane

Dan wasan kungiyar Tottenham Harry Kane ya ce yana so ya wuce bajintar cin kwallayen dan wasan Barcelona Lionel Messi.


Kane, mai shekara 25, kungiyarsa za ta fafata ne da Barcelona a ranar Laraba a gida a wasan rukunin B na Gasar Zakarun Turai.

"Messi yana shigewa gaba wajen nuna bajinta hakan kuma yana ba ni kwarin gwiwar kara zage damtse," in ji Kane.

"Ina fatan wata rana zan ci kwallaye da yawa, idan ban ma wuce dan wasan ba ke nen."
Dan kwallon Ingilan shi ne ya fi kowa zura kwallaye a raga a kakar wasanni ukun gasar firimiya da suka gabata kuma shi ne wanda ya fi cin kwallaye a Gasar Cin Kofin Duniya wadda aka yi bana a kasar Rasha.

A karshen makon jiya ne adadin kwallayen da dan wasan ya zura a raga suka kai 145 a lokacin wasansu da Huddersfield.

Sai dai Kane yana bayan Messi wanda ya zura kwallaye 560 a raga, kuma ya zura guda 103 ne a Gasar Zakarun Turai.

"Messi da Cristiano Ronaldo su ne 'yan wasan da suke cin kwallaye 50 zuwa 60 a kowace kaka," in ji Kane.
BBChausa.

No comments:

Post a Comment