Monday, 8 October 2018

John Terry ya yi ritaya daga buga tamaula

Tsohon dan wasan Ingila da kungiyar Chelsea John Terry ya yi ritaya daga buga tamaula.
Terry, mai shekara 37, ya kasance ba shi da kungiya tun bayan barin kungiyar Aston Villa a bana.


Dan kwallon wanda ya bayyana ritayarsa a shafinsa na Instagram yana cewa: "Bayan na shafe shekara 23 a matsayin dan kwallon kafa, ina ganin yanzu lokaci ya yi da zan yi ritaya daga buga wasa."
Terry, wanda sau 78 yana taka wa Ingila leda, ya bar kungiyar Chelsea ne a shekarar 2017 bayan ya shafe kimanin shekara 20 a kungiyar.
Sau biyar yana lashe kofin gasar firimiya da kofunan gasar FA biyar da kuma Gasar Zakarun Turai duka a kungiyar Chelsea.
Hakazalika dan wasan ya lashe kofunan lig biyar da kofin Gasar Europa a wasanni fiye da 700 da ya yi wa Chelsea.
Terry ya yi kakar 2017-18 ne a kungiyar Aston Villa, kuma ya yi wasan karshe ne a wasan da kungiyar ta doke Fulham da ci 1-0 a watan Mayu.
Ya bar kungiyar Aston Villa ne bayan da kwangilarsa ta kare da kungiyar, amma sai ya ki karbar tayin komawa Spartak Moscow a watan jiya.
BBChausa.

No comments:

Post a Comment