Wednesday, 24 October 2018

Kada bayyanar Kanu ta tayar muku da hankali>>Fadar shugaban kasa ga 'yan Najeriya

Gwamnatin tarayya ta mayar da martani akan wani bidiyo da ya bayyana dake nuna cewa shugaban masu fafutikar kafa kasar Biafra, Nnamdi Kanu na nan da ranashi inda aka nunashi ya bayyana a kasar Isra'ila, tace kada hakan ya damu 'yan Najeriya ba abin tada hankali bane domin gwamnati na ci gaba da kare iyakokinta yanda ya kamata.


A wata sanarwa da me magana da yawun shugaba kasa, Garba Shehu ya fitar yace Najeriya zata ci gaba da kulla huldar dangantaka da kasashen Duniya kuma barazanar Nnamdi Kanu kada ta tayar da hankali, Gwamnatin na jiran dawowarshi kasar.

A wata hira da yayi da BBC, Garba Shehu ya bayyana cewa bayyanar Kanu ya wanke zargin gwamnati da ake yi na cewa itace ta batar dashi.

No comments:

Post a Comment